Tuesday, February 27, 2024
HomenewsZimbabwe ta fara gangamin rigakafin kwalara bayan cutar ta kashe mutane 452

Zimbabwe ta fara gangamin rigakafin kwalara bayan cutar ta kashe mutane 452


Zimbabwe ta kadamar da gangamin rigakafin cutar cholera ko kuma amai da gudawa wanda ke da nufin yiwa mutum fiye da miliyan 2  rigakafin a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar wadda ta kasha daruruwan mutane tun bayan barkewarta a bara.

Wallafawa ranar:

Minti 1

Alkaluman ma’aikatar lafiya ta Zimbabwe na nuna yadda annobar cutar ta cholera ta kashe mutane 452 cikin mutum dubu 20 da 446 da suka harbu da ita daga watan Fabarirun bara zuwa bana.

Ma’aikatar lafiyar ta bayyana cewa galibin masu harbuwa da cutar ta cholera kananan yara, wannan dalili ya tilasta daukar matakin rigakafin don basu kariya.

Zimbabwe za ta karbi alluran rigakafin cholera miliyan 2 da dubu 300 daga asusun UNICEF da hukumar lafiya ta WHO alluran da kasar za ta rarraba zuwa yankuna 29 da cutar tafi tsananta.

A cewar ma’aikatar lafiyar tuni allurai dubu 892 suka isa gareta kuma su ne ta fara gangamin rigakafinsu tun a jiya Litinin.Source link

RELATED ARTICLES

Leave a reply

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -

Most Popular

Recent Comments